3 Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4 Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.
5-6 Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
7 Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.
8 Zai cika alkawarinsa har abada,Alkawaransa kuma don dubban zamanai,
9 Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.
10 Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,