30 Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.
31 Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.
32 Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.
33 Ya lalatar da 'ya'yan inabinsu da itatuwan ɓaurensu,Ya kakkarya itatuwansu.
34 Ya ba da umarni, sai fāri suka zo,Dubun dubbai da ba su ƙidayuwa.
35 Suka cinye dukan tsire-tsire na ƙasa.Suka cinye dukan amfanin gonaki.
36 Ya karkashe dukan 'ya'yan fari mazaNa dukan iyalan Masarawa.