1 Ku yabi Ubangiji!Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi,Ƙaunarsa madawwamiya ce.
2 Wa zai iya faɗar dukan manya manyan ayyuka da ya yi?Wa zai iya yi masa isasshen yabo?
3 Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa,Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!
4 Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji!Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.