16 Can cikin hamada suka ji kishin MusaDa Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,
17 Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan,Ta binne Abiram da iyalinsa.
18 Wuta ta sauko bisa magoya bayansu,Ta ƙone mugayen mutanen nan.
19 Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb,Suka yi masa sujada.
20 Suka musaya ɗaukakar AllahDa siffar dabba mai cin ciyawa.
21 Suka manta da Allah wanda ya cece su,Ta wurin manyan ayyuka da ya yi a Masar.
22 Kai, Allah ya aikata abubuwa masu ban al'ajabi a can!Ga kuma abubuwa masu banmamaki da ya aikata a Bahar Maliya!