25 Suka zauna cikin alfarwansu suna ta gunaguni,Sun ƙi su saurari Ubangiji.
26 Saboda haka ya yi musu kakkausan kashedi,Cewa shi zai sa su duka su mutu a jejin,
27 Zai warwatsa zuriyarsu a cikin arna,Ya bar su su mutu a baƙuwar ƙasa.
28 Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor,Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.
29 Suka tsokani Ubangiji, ya yi fushi saboda ayyukansu,Mugawar cuta ta auka musu,
30 Amma Finehas ya tashi, ya yanke hukunci a kan laifin,Aka kuwa kawar da annobar.
31 Tun daga lokacin nan ake ta tunawa da shi,Saboda abin da ya yi.Za a yi ta tunawa da shi a dukan zamanai masu zuwa.