1 Ku gode wa Ubangiji, gama shi nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce!
2 Ku zo mu yabi Ubangiji tare,Dukanku waɗanda ya fansa,Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.
3 Ya komo da ku daga ƙasashen waje,Daga gabas da yamma, kudu da arewa.
4 Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.