18 Ba su so su ga abinci,Sun kusa mutuwa.
19 A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.
20 Da umarninsa ya warkar da su,Ya cece su daga kabari.
21 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
22 Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu,Su raira waƙoƙin murna,Su faɗi dukan abin da ya yi!
23 Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage,Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.
24 Suka ga abin da Ubangiji ya aikata,Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.