2 Ku zo mu yabi Ubangiji tare,Dukanku waɗanda ya fansa,Gama ya ƙwato ku daga maƙiyanku.
3 Ya komo da ku daga ƙasashen waje,Daga gabas da yamma, kudu da arewa.
4 Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.
5 Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa,Suka fid da zuciya ga kome.
6 Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
7 Ya fisshe su, ya bi da su sosai,Zuwa birnin da za su zauna.
8 Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!