28 Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabarsu.
29 Ya sa hadiri ya yi tsit,Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.
30 Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru,Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya,Wurin da suke so.
31 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.
32 Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a,Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.
33 Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.
34 Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.