40 Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa.Ya sa su suka yi ta kai da kawowaA hamada inda ba hanya.
41 Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu,Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.
42 Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna,Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.
43 Da ma a ce masu hikimaZa su yi tunani a kan waɗannan abubuwa,Da ma kuma su yardaDa madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.