9 Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa,Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.
10 Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa,'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,
11 Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki,Sun kuwa ƙi koyarwarsa.
12 Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki,Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.
13 A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.
14 Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa,Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.
15 Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.