2 Ku farka, ya molona da garayata!Zan farkar da rana!
3 Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!
4 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai,Amincinka kuma ya kai sararin sammai.
5 Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6 Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.
7 A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,“Da nasara zan raba Shekem,Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
8 Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,Ifraimu ne kwalkwalina,Yahuza kuma sandana ne na sarauta.