1 Ina yabonka, ya Allah, kada ka yi shiru!
2 Mugaye da maƙaryata sun tasar mini,Suna ta faɗar ƙarairayi a kaina.
3 Suna faɗar mugayen abubuwa a kaina.Suna tasar mini ba dalili.
4 Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu,Har ina yi musu addu'a.