25 Sa'ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba'a,Suna kaɗa kai saboda raini.
26 Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna,Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!
27 Ka sa maƙiyana su sani,Kai ne Mai Cetona.
28 Watakila su la'anta ni,Amma kai za ka sa mini albarka,Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini.Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.
29 Ka sa kunya ta rufe maƙiyana,Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.
30 Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya.Zan yabe shi a taron jama'a,
31 Saboda yakan kāre talaka,Domin ya cece shi daga waɗandaSuka sa masa laifin mutuwa.