5 Sukan sāka mini alheri da mugunta,Sukan sāka mini ƙauna da ƙiyayya.
6 Ka zaɓi lalataccen mutum ya shara'anta maƙiyina,Ka sa ɗaya daga cikin maƙiyansaYa gabatar da ƙararsa.
7 Ka sa a same shi da laifi a shari'ar da ake yi masa,Ka sa har addu'ar da yake yiTa zama babban laifi!
8 Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan,Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!
9 Ka sa 'ya'yansa su zama marayu,Matarsa kuwa ta zama gwauruwa!
10 Ka sa 'ya'yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara.Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!
11 Ka sa waɗanda suke binsa bashi su kwasheDukan abin da yake da shi.Ka sa baƙi su kwashe dukan abin da ya sha wahalar nema.