1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Zan yi wa Ubangiji godiya da zuciya ɗaya,A cikin taron jama'arsa.
2 Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa!Duk waɗanda suke murna da suSuna so su fahimce su.
3 Dukan abin da yake yi,Cike yake da girma da ɗaukaka,Adalcinsa har abada ne.
4 Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba,Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.
5 Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci,Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.
6 Ya nuna ikonsa ga jama'arsaSaboda ya ba su ƙasashen baƙi.
7 Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.Dukan umarnansa, abin dogara ne.