3 Dukan abin da yake yi,Cike yake da girma da ɗaukaka,Adalcinsa har abada ne.
4 Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba,Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.
5 Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci,Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.
6 Ya nuna ikonsa ga jama'arsaSaboda ya ba su ƙasashen baƙi.
7 Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.Dukan umarnansa, abin dogara ne.
8 Sukan tabbata har abada,Da gaskiya da adalci aka ba da su.
9 Ya kawo wa jama'arsa ceto,Ya kuma yi musu madawwamin alkawari.Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!