3 Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya,Adalcinsa zai tabbata har abada.
4 Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu,Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.
5 Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.
6 Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,Ba za a taɓa mantawa da shi ba.
7 Ba ya tsoron jin mugun labari,Bangaskiyarsa tana da ƙarfi,Ga Ubangiji yake dogara.
8 Ba shi da damuwa ko tsoro,Ya tabbata zai ga faɗuwar maƙiyansa.
9 Yakan bayar ga matalauta hannu sake,Alherinsa kuwa dawwamamme ne.Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.