1 Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar,Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,
2 Yahuza ya zama tsattsarkar jama'ar Ubangiji,Isra'ila ya zama abin mallakarsa.
3 Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu,Kogin Urdun ya daina gudu.
4 Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki,Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.