5 Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu?Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu?
6 Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki?Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle,Kuna kewayawa kamar tumaki?
7 Ki yi rawar jiki, ya ke duniya,Saboda zuwan Ubangiji,A gaban Allah na Yakubu,
8 Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa,Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai,Masu bulbulo da ruwa.