1 A gare ka kaɗai, ya Ubangiji,A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba,Dole a girmama ka,Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
2 Me ya sa sauran al'umma suke tambayarmu,“Ina Allahnku?”
3 Allahnmu yana Sama,Yana aikata yadda yake so.
4 Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne,Da hannu aka siffata su.
5 Suna da baki, amma ba sa magana,Suna da idanu, amma ba sa gani.
6 Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.
7 Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome,Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya.Ba su da murya sam.