4 Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne,Da hannu aka siffata su.
5 Suna da baki, amma ba sa magana,Suna da idanu, amma ba sa gani.
6 Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.
7 Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome,Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya.Ba su da murya sam.
8 Ka sa waɗanda suka yi su,Da dukan masu dogara gare su,Su zama kamar gumakan da suka yi!
9 Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.
10 Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.