1 Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina,Yana kasa kunne ga addu'o'ina.
2 Yakan kasa kunne gare ni,A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam,Razanar kabari ta auka mini,Na cika da tsoro da alhini.
4 Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
5 Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.