2 Yakan kasa kunne gare ni,A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam,Razanar kabari ta auka mini,Na cika da tsoro da alhini.
4 Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
5 Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.
6 Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.
7 Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
8 Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.