6 Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.
7 Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
8 Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.
9 Don haka nake tafiya a gaban UbangijiA duniyar masu rai.
10 Na dai yi ta gaskatawa, ko da yakeNa ce, “An ragargaza ni sarai.”
11 Sa'ad da na ji tsoro na ce,“Ba wanda za a iya dogara gare shi.”
12 Me zan bayar ga UbangijiSaboda dukan alheransa gare ni?