14 Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,Shi ne Mai Cetona!
15 Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasaraA cikin alfarwan jama'ar Allah.“Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!
16 Ikonsa ne ya kawo mana nasara,Babban ikonsa a wurin yaƙi!”
17 Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.
18 Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,Amma bai kashe ni ba.
19 A buɗe mini ƙofofin Haikali,Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!
20 Wannan ƙofar Ubangiji ce,Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!