17 Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.
18 Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,Amma bai kashe ni ba.
19 A buɗe mini ƙofofin Haikali,Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!
20 Wannan ƙofar Ubangiji ce,Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!
21 Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni,Domin ka ba ni nasara!
22 Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani,Sai ya zama shi ya fi duka amfani.
23 Ubangiji ne ya yi haka,Wannan kuwa abin banmamaki ne!