2 Bari jama'ar Isra'ila su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
3 Bari dukan firistoci na Allah su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
4 Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
5 A cikin wahalata na yi kira ga UbangijiYa kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.
6 Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba.Me mutane za su iya yi mini?
7 Ubangiji ne yake taimakona,Zan kuwa ga fāɗuwar maƙiyana da idona.
8 Gwamma a dogara ga Ubangiji,Da a dogara ga mutane.