26 Allah yakan sa wa wanda ya zo da sunan Ubangiji albarka!Daga Haikalin Ubangiji muke yabonka!
27 Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri,Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi,Ku ɗaura su a zankayen bagade.
28 Kai ne Allahna, kai nake yi wa godiya,Zan yi shelar girmanka.
29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne,Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.