8 Gwamma a dogara ga Ubangiji,Da a dogara ga mutane.
9 Gwamma a dogara ga Ubangiji,Da a dogara ga shugabanni na mutane kawai.
10 Ma ƙiya da yawa sun kewaye ni,Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
11 Suka kewaye ni a kowane gefeAmma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!
12 Suka rufe ni kamar ƙudan zuma,Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji,Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!
13 Aka auko mini da tsanani,Har aka kore ni,Amma Ubangiji ya taimake ni.
14 Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,Shi ne Mai Cetona!