1 Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu,Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.
2 Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa,Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.
3 Hakika ba su yin laifi,Sukan yi tafiya a hanyoyin Ubangiji.
4 Kai ka ba mu dokokinka,Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.
5 Na sa zuciya zan yi aminci,Game da kiyaye dokokinka!
6 Idan na kula da dukan umarnanka,To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.