102 Ban raina koyarwarka baSaboda kai ne ka koya mini.
103 Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi,Har sun fi zuma zaƙi!
104 Na ƙaru da hikima daga dokokinka,Saboda haka ina ƙin dukan halin da yake ba daidai ba.
105 Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,Haske ne kuma a kan hanyata.
106 Zan cika muhimmin alkawarina,In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.
107 Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa,Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!
108 Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,Ka koya mini umarnanka.