105 Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni,Haske ne kuma a kan hanyata.
106 Zan cika muhimmin alkawarina,In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.
107 Azabaina, ya Ubangiji, suna da yawa,Ka rayar da ni kamar yadda ka alkawarta!
108 Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,Ka koya mini umarnanka.
109 Kullum a shirye nake in kasai da raina,Ban manta da umarninka ba.
110 Mugaye sun kafa mini tarko,Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
111 Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.