108 Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,Ka koya mini umarnanka.
109 Kullum a shirye nake in kasai da raina,Ban manta da umarninka ba.
110 Mugaye sun kafa mini tarko,Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.
111 Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.
112 Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka,Har ranar mutuwata.
113 Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci,Amma ina ƙaunar dokarka.
114 Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni,Ina sa zuciya ga alkawarinka.