112 Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka,Har ranar mutuwata.
113 Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci,Amma ina ƙaunar dokarka.
114 Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni,Ina sa zuciya ga alkawarinka.
115 Ku rabu da ni, ku masu zunubi!Zan yi biyayya da umarnan Allahna.
116 Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu,Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!
117 Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya,Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.
118 Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka,Dabarunsu na yaudara banza ne.