118 Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka,Dabarunsu na yaudara banza ne.
119 Kakan yi banza da duk mai mugunta,Don haka ina ƙaunar koyarwarka.
120 Saboda kai, nake jin tsoro,Na cika da tsoro saboda shari'unka.
121 Na yi abin da yake daidai mai kyau,Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!
122 Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka,Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!
123 Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka,Ceton da ka alkawarta.
124 Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,Ka koya mini umarnanka.