122 Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka,Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!
123 Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka,Ceton da ka alkawarta.
124 Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,Ka koya mini umarnanka.
125 Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa,Don in san koyarwarka.
126 Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
127 Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,Fiye da zinariya tsantsa.
128 Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.