126 Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!
127 Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,Fiye da zinariya tsantsa.
128 Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.
129 Koyarwarka tana da ban al'ajabi,Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.
130 Fassarar koyarwarka takan ba da haske,Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.
131 Ina haki da baki a buɗe,Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.
132 Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai,Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.