133 Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta,Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.
134 Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata,Domin in yi biyayya da umarnanka.
135 Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni,Ka koya mini dokokinka.
136 Hawayena suna malalowa kamar kogi,Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.
137 Kai mai adalci ne, ya Ubangiji,Dokokinka kuma daidai ne,
138 Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,Daidai ne kuwa.
139 Fushi yana cina kamar wuta,Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.