140 Alkawarinka ba ya tashi!Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!
141 Ni ba kome ba ne, rainanne ne,Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.
142 Adalcinka zai tabbata har abada,Dokarka gaskiya ce koyaushe.
143 A cike nake da wahala da damuwa,Amma umarnanka suna faranta zuciyata.
144 Koyarwarka masu adalci ne har abada,Ka ba ni ganewa domin in rayu.
145 Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,Ka amsa mini, ya Ubangiji,Zan yi biyayya da umarnanka!
146 Ina kira gare ka,Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!