145 Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,Ka amsa mini, ya Ubangiji,Zan yi biyayya da umarnanka!
146 Ina kira gare ka,Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!
147 Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako,Na sa zuciya ga alkawarinka.
148 Dare farai ban yi barci ba,Ina ta bimbini a kan koyarwarka.
149 Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka,Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!
150 Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa,Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.
151 Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji,Dukan alkawaranka gaskiya ne.