151 Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji,Dukan alkawaranka gaskiya ne.
152 Tuntuni na ji labarin koyarwarka,Ka sa su tabbata har abada.
153 Ka dubi wahalata, ka cece ni,Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.
154 Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
155 Ba za a ceci mugaye ba,Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.
156 Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.
157 Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.