154 Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
155 Ba za a ceci mugaye ba,Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.
156 Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.
157 Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.
158 Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana,Sai in ji ƙyama ƙwarai,Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.
159 Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
160 Cibiyar dokarka gaskiya ce,Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.