160 Cibiyar dokarka gaskiya ce,Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.
161 Ƙarfafan mutane sun auka mini ba dalili,Amma maganarka ce nake girmamawa.
162 In farin ciki ƙwarai saboda alkawaranka,Farin cikina kamar na wanda ya sami dukiya mai yawa ne.
163 Ina ƙin ƙarairayi, ba na jin daɗinsu,Amma ina ƙaunar dokarka.
164 A kowace rana nakan gode maka sau bakwai,Saboda shari'unka masu adalci ne.
165 Waɗanda suke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,Ba wani abin da zai sa su fāɗi.
166 Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,Ina aikata abin da ka umarta.