166 Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji,Ina aikata abin da ka umarta.
167 Ina biyayya da ka'idodinka,Ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.
168 Ina biyayya da umarnanka da koyarwarka,Kana kuwa ganin dukan abin da nake yi.
169 Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji!Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.
170 Bari addu'ata ta zo gare ka,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
171 Zan yabe ka kullayauminDomin ka koya mini ka'idodinka.
172 Zan raira waƙa a kan alkawarinka,Domin umarnanka a gaskiya ne.