169 Bari kukana yă kai gare ka, ya Ubangiji!Ka ganar da ni kamar yadda ka alkawarta.
170 Bari addu'ata ta zo gare ka,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!
171 Zan yabe ka kullayauminDomin ka koya mini ka'idodinka.
172 Zan raira waƙa a kan alkawarinka,Domin umarnanka a gaskiya ne.
173 Kullum a shirye kake domin ka taimake ni,Saboda ina bin umarnanka.
174 Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji!Ina samun farin ciki ga dokarka.
175 Ka rayar da ni don in yabe ka,Ka sa koyarwarka su taimake ni!