27 Ka koya mini yadda zan yi biyayya da dokokinka,In kuma yi nazarin koyarwarka mai banmamaki.
28 Ɓacin rai ya ci ƙarfina,Ka ƙarfafa ni, kamar yadda ka alkawarta.
29 Ka kiyaye ni daga bin muguwar hanya,Ta wurin alherinka, ka koya mini dokarka.
30 Na yi niyya in yi biyayya,Na mai da hankali ga ka'idodinka.
31 Na bi umarnanka, ya Ubangiji,Kada ka sa in kasa ci wa burina!
32 Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka,Gama za ka ƙara mini fahimi.
33 Ka koya mini ma'anar dokokinka, ya Ubangiji,Zan kuwa yi biyayya da su a kowane lokaci.