34 Ka fassara mini dokarka, ni kuwa zan yi biyayya da ita,Zan kiyaye ta da zuciya ɗaya.
35 Ka bishe ni a hanyar umarnanka,Domin a cikinsu nakan sami farin ciki
36 Ka sa ni in so yin biyayya da ka'idodinka,Fiye da samun dukiya.
37 Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani,Ka yi mini alheri kamar yadda ka alkawarta.
38 Ka tabbatar da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,Irin wanda kakan yi wa waɗanda suke tsoronka.
39 Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro,Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!
40 Ina so in yi biyayya da umarnanka,Gama kai mai adalci ne,Ka yi mini alheri!