39 Ka kiyaye ni daga cin mutuncin da nake tsoro,Ka'idodinka suna da amfani ƙwarai!
40 Ina so in yi biyayya da umarnanka,Gama kai mai adalci ne,Ka yi mini alheri!
41 Ka nuna mini yawan ƙaunar da kake yi mini, ya Ubangiji,Ka cece ni bisa ga alkawarinka.
42 Sa'an nan zan amsa wa waɗanda suke cin mutuncina,Domin na dogara ga maganarka.
43 Ka ba ni iko in iyar da saƙonka na gaskiya a kowane lokaci,Gama sa zuciyata tana ga hukuntanka.
44 Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!
45 Zan rayu da cikakken 'yanci,Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.