4 Kai ka ba mu dokokinka,Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.
5 Na sa zuciya zan yi aminci,Game da kiyaye dokokinka!
6 Idan na kula da dukan umarnanka,To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.
7 Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
8 Zan yi biyayya da dokokinka,Ko kusa kada ka kashe ni!
9 Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?Sai ta wurin biyayya da umarnanka.
10 Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!